Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta ce tana maraba da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf zuwa cikinta, inda ta ce a shirye take ta karɓe shi.
Ta cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na Kano Abdullahi Abbas ya fitar, ya ce za su ba gwamnan goyon baya, sannan ya nanata muhimmancin haɗin kai da ci gaban jam’iyyar a faɗin jihar Kano baki ɗaya.
Abdullahi Abbas ya ce jam’iyyar na buƙatar haɗin kai da zaman lafiya da girmama juna, sannan ya ƙara da cewa yunƙurin shigowar Gwamna Abba cikin APC na ƙara nuna ƙwarewar Tinubu a siyasa, wadda ke sa jam’iyyun hamayya ke ƙara sha’awar shiga jam’iyyarsa.








