Home Labarai Majalisar Ƙaramar hukumar Dala ta Haramta yin kiɗan Gangi

Majalisar Ƙaramar hukumar Dala ta Haramta yin kiɗan Gangi

0

Majalisar ƙaramar hukumar Dala, ta haramta yin duk wani wasa a lokacin bukukuwan aure musamman ma kiɗan Gangi a fadin karamar hukumar, sakamakon yadda wasu ɓata garin matasa ke fakewa da hakan suna tayar da hankalin jama’a.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Suraj Ibrahim Imam, ne ya sanar da ɗaukar wannan mataki yayin zama da masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar a daren yau Laraba.

Ɗaukar matakin dai ya biyo bayan yadda wasu ɓata garin matasa da aka hana yin kiɗan Gangi suka banka wa gidan mai unguwa Wuta a daren ranar Talatar makon nan a unguwar Rijiya biyu da ke yankin ƙaramar hukumar.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka samu wasu bata-gari da aka hana su yin wasan kauraye na kidan gangi a unguwar Rijiya Biyu, inda daga bisani suka dawo cikin dare suka kunna wuta a gidan Mai Unguwar yankin.

Shugaban Karamar Hukumar ta Dala, Suraj Ibrahim Imam, ya ce ba za su saurara wa duk wanda aka samu da hannu wajen aikata ɓarnar ba.

Haka kuma, bukaci mazauna ƙaramar hukumar da su basu cikakken haɗin kai domin ganin irin wannan ɓarna ba ta sake faruwa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here