Kotun Masana’antu ta Najeriya shiyyar birnin tarayya Abuja, ta bayar da umarnin hana ƙungiyar Likitocin masu neman ƙwarewa NARD ta da mambobinta shiga yajin aikin da suka shirya farawa daga makon gobe.
Kotun ta ce ba a yarda ƙungiyar ko kowane membanta su ɗauki wannan mataki na yajin aiki ba har sai an saurari ƙarar da ke gaban kotu.
Alkalin kotun, Emmanuel Subilim, ne ya bayar da wannan umarni yayin yanke hukunci kan wata bukata ta gaggawa da gwamantin tarayya da babban lauyan gwamnatin tarayya suka shigar.
Hukuncin ya biyo bayan bayanan da daraktar shari’o’in farar hula a ma’aikatar shari’a ta tarayya, Maimuna Lami Shiru, ta gabatar tare da tawagar lauyoyin gwamnati.
Wadanda aka sanya a matsayin wadanda ake kara a cikin bukatar dakararwar sun hada da Ƙungiyar Likitocin da shugabanta na ƙasa Mohammad Suleman, da babban sakataren ƙungiyar Shuaibu Ibrahim.
Ƙungiyar ta sanar da shirin komawa wani yajin aiki na sai Baba ta gani bayan da ta zargi gwamantin tarayya da gaza aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma tsakaninta da likitocin.
Haka kuma, ƙungiyar ta ce, gazawa wajen aiwatar da yarjejeniyar fahimta da aka sanya hannu da ma’aikatar lafiya ta tarayya da gwamantin tarayya, duk da cikar wa’adin da aka kayyade, ne ya sa yajin aikin ya zama dole.
Ta kuma bayyana cewa an umarci shugabannin cibiyoyin ƙungiyar a duk fadin kasar su gudanar da tarukan mambobi da kuma bayani ga manema labarai a matsayin shiri na daukar mataki.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa za a gudanar da zanga-zangar cikin asibitoci da cibiyoyin aiki, sannan daga bisani a wuce zuwa matakin zanga-zangar shiyya-shiyya da kuma ta ƙasa baki ɗaya.
Daga cikin bukatun da ƙungiyar ke nema akwai dawo da wasu likitocin masu neman ƙwarewa da aka kora, biyan bashin albashi da karin girma, cikakken aiwatar da alawus-alawus na horo, warware matsalolin albashin likitocin, sake tsara matsayin mambobi bayan jarabawa, da kuma ci gaba da tattaunawar yarjejeniyar aiki tsakanin ƙungiyar da gwamantin tarayya.
Solacebase








