Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta NDLEA ta ce, ta sake cafke wani dattijo mai shekaru 80, mai suna Jeremiah Isaiah Nkanta, bisa zargin komawa harkar fataucin miyagun ƙwayoyi, kusan shekaru uku bayan kammala zaman gidan yari saboda irin wannan laifi da aka kama shi da shi a baya.
A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da kan jama’a na hukumar Mista Femi Babafemi ya fitar a ƙarshen makon nan, Jeremiah Isaiah Nkanta, wanda ya shahara wajen dillancin miyagun ƙwayoyi, an fara kama shi ne a ranar 14 ga Disamban shekarar 2022, inda Kotun Tarayya da ke Uyo, Jihar Akwa Ibom, ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, Sai dai bayan fitowarsa, rahotanni sun nuna cewa ya koma tsohuwar ɗabi’arsa.
Hukumar ta kuma ce, Bisa bayanan sirri da jami’anta suka samu, ne ya kai su ga sake cafke shi a ranar Asabar, 10 ga watan nan da muke ciki na Janairu a gidansa da ke ƙauyen Mmanta da ke yankin Ƙaramar Hukumar Abak ta Jihar Akwa Ibom, inda aka same shi da kilogiram 5 da ɗigo 7 na tabar wiwi.
Hukumar ta ce, wa wani Kamen na daban kuma, jami’anta sun cafke wani ɗan kasuwa mai shekaru 37, mai suna Ani Onyebuchi Romans, a kan hanyar Oron zuwa Ibaka, yayin da yake ƙoƙarin kai ƙwayoyin tramadol zuwa ƙasar Kamaru Inda aka gano cewa ya ɓoye ƙwayoyin Tramadol masu nauyin kilogiram 5 da ɗigo 3 a cikin tufafin wasu mutummutumi da yake ɗauke da su.
Sanarwar, ta kuma ce, A wasu jihohi kuwa, NDLEA ta cafke manyan dillalan miyagun ƙwayoyi tare da ƙwace tarin kayan maye a Oyo da Edo da Niger da Taraba da Adamawa, ciki har da nau’o’in tabar wiwi daban-daban da ƙwayoyin tramadol da kuma kuɗaɗen da ake zargin kuɗin haramtacciyar sana’ar ne.
Haka kuma ta cikin sanarwar, Mista Femi Babafemi, ya ƙara da cewa, hukumar ta NDLEA na ci gaba da yaƙi da shan da fataucin miyagun ƙwayoyi, tare da ƙara shirye-shiryen Wayar da Kai mai laƙabin WADA a makarantu da wuraren ibada ga al’umma a faɗin Najeriya.








