Home Labarai Hukumar Yaƙi da Fasa Kwauri ta Najeriya ta fara aiki da sabon...

Hukumar Yaƙi da Fasa Kwauri ta Najeriya ta fara aiki da sabon tsarin fiton kayayyaki

0

Hukumar Kwastam ta din ta Najeriya, ta sanar da fara aiwatar da sabon tsarin aiki domin daidaita ayyukan kamfanonin jigilar kai kayayyaki da ke aiki a tsarin da mai aikawa ke ɗaukar nauyin dukkan kuɗin haraji da sauran cajikunji-kunji kafin kaya su isa ga mai karɓa.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, na kasa Abdullahi Maiwada, mai mukammin mataimakin kwanturola a hukuma ya fitar ya ce sabon shirin zai samar da tsari guda na rijista, gabatar da bayanan kaya da bayyana su da kimanta su har zuwa lokacin da za su fita daga hannun hukumar ta kwastam da kuma kai su ga mai karɓa, da kuma sanya ido kan bin doka, daidai da ƙa’idojin da ake amfani da su a duniya.

A cewarsa, ƙarƙashin sabon tsari, duk kamfanin kai kaya da ke son aiki a wannan tsari dole ne ya samu lasisi daga sashen bayar da lasisi da izini na da ke shalkwatar hukumar kwastam, ƙarƙashin sashen haraji da ciniki.

Ya ce, dole ne kamfanonin su miƙa dukkan takardun da ake buƙata, ciki har da takardun rajista na Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni da ingantaccen lasisin aikin isar da kaya sai takardar lamuni ta bin doka, da kuma rubutacciyar buƙata ta neman izinin aiki a tsarin.

Maiwada ya bayyana cewa duk kamfanonin da aka ba lasisi dole ne su miƙa bayanan kayan da aka shigo da su ta na’urar Kwamfuta awanni ashirin da huɗu kafin isowar kaya, tare da bayyanawa a fili cewa mai tura kaya ya biya dukkan haraji.

Haka kuma dokar ta wajabta cewa, sai bayanan su haɗa da cikakken bayanin nau’in kaya da kimarsu da madaukinsu da kuma wurin da suka fito da sunan mai karɓa, bisa ƙa’idojin Hukumar Kwastam ta Duniya ta tanada.

Ya ƙara da cewa sabon tsarin ya wajabta wa kamfanonin dakon kaya su kasance masu bayyana kaya da kansu ta hanyar cike takardar bayanin kaya ta fasahar zamani a shafin da hukumar kwastam ke amfani da shi.

A cewarsa, dole ne bayanan su haɗa da ƙimar kaya kafin jigila, tare da takardun saye, takardar jigilar jirgi, da jerin kaya.
“Haka kuma, dole ne a kammala biyan dukkan harajin kwastam, harajin ƙarin kima, da sauran kuɗaɗen da doka ta tanada ta hanyoyin biyan kuɗi da hukumar kwastam ta amince da su kafin a fitar da kaya.

Sannan kuma za’a rika duba kaya bisa tantance haɗari, inda za a yi cikakken bincike idan an gano sabani ko alamar haɗari,” in ji shi.

Ya jaddada cewa ba a yarda a kai kaya ga mai karɓa ba sai bayan an kammala dukkan matakan fitarwa, kuma dole ne a bayar da shaidar kai kaya idan hukumar ta buƙata.

Maiwada ya ce, domin tabbatar da bin doka, hukumar kwastam ta kafa tsauraran hanyoyin sa ido ta hanyar bincike bayan an fitar da kaya lokaci zuwa lokaci.

Ya bayyana cewa waɗannan bincike za su tabbatar da sahihancin bayanan da aka bayar, hana asarar kuɗaɗen shiga, da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin rarrabawa da kimanta kaya.

Ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya karya doka, kamar bayar da bayanan ƙarya, kin biyan haraji, ko rashin ɗa’a a aiki, zai fuskanci hukunci da suka haɗa da dakatarwa ko kwace lasisin aiki, ƙwace kaya, tara da ƙarin kuɗi, da kuma gurfanarwa a gaban shari’a bisa dokar hukumar kwastam ta shekarar 2023.

Ya kuma ce, an wajabta wa kamfanonin isar da kaya su rika miƙa rahoton wata-wata na dukkan jigilar kaya da aka gudanar a wannan tsari, ciki har da bayanan biyan haraji, rarrabuwar kaya, da shaidar kai kaya, ga sassan hukumar da abin ya shafa.

A ƙarshe, Maiwada ya ce da wannan mataki, hukumar kwastam ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa gaskiya da tsari na fitar da kaya, ƙara kare kuɗaɗen shiga na gwamnati, sauƙaƙa halastaccen ciniki, da tabbatar da cewa ayyukan kamfanonin isar da kaya suna tafiya bisa mafi girman ƙa’idojin duniya.

Haka kuma a cewar mai magana da yawun hukumar ta Kwastam na kasa, Sabon tsarin ya na da tushe ne a ƙa’idojin cinikayya na duniya na shekarar 2020, dokokin hukumar kwastam ta Najeriya, ƙa’idojin Hukumar Kwastam ta Duniya, yarjejeniyar sauƙaƙa harkokin kasuwanci ta duniya, da dokokin hukumar gidan waya ta Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here