Home Labarai Gwamnatin Kano ta sha alwashin inganta aikin Jarida tare da ganin ana...

Gwamnatin Kano ta sha alwashin inganta aikin Jarida tare da ganin ana yinsa bisa ƙa’ida

0

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa aikin jarida mai nagarta da ɗa’a, musamman a fagen jaridar Internet.

Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya samu wakilcin Kwamishinan ma’aikatar yaɗa labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron horaswa na kwana biyu ga masu wallafa labarai a jaridun Intanet na Kano.

Taron, wanda shi ne irinsa na farko da Kano Online Chapel na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) ta shirya wanda Ma’aikatar yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kano ta ɗauki nauyinsa aka fara gudanar da shi a birnin Dutse na jihar Jigawa a yau Laraba.

Da ya ke buɗe taron, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki na sake tsarawa da ɗaukaka aikin jaridar ƙafar Internet a matsayin ginshiƙi a aikin kafafen yaɗa labarai na zamani.

Haka kuma, ya ce, taron ya nuna yadda Gwamnatin Kano ke fahimtar tasirin da jaridar Internet ke ƙara samu, tare da buƙatar bai wa ‘yan jarida kayan aiki da ilimi da horo yadda ya dace domin tafiya da sauye-sauyen da ke faruwa a duniyar yaɗa labarai.

Kwamishinan ya yaba wa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa amincewa da ɗaukar nauyin horon, yana mai cewa hakan shaida ce ta kyakkyawan jagoranci da kuma jajircewar gwamnatinsa wajen bunƙasa aikin jarida a Kano.

Ya ƙara da cewa ‘yan jaridar na ƙafar Internet su ne tushen gudanar da aikin jarida a nan gaba, inda ya buƙace su da su rungumi tsarin gudanar da aiki bisa gaskiya da ƙwarewa da kauce wa ƙirƙirar labaran tayar da hankali, tare da bambance aikin jarida na gaskiya da harkokin kafafen sada zumunta marasa tsari.

A ƙarshe, Kwamared Waiya ya tabbatar da ci gaba da goyon bayan gwamnati ga ‘yancin faɗin albarkacin baki da aikin jarida mai inganci tare da bayyana yunƙurin kafa Dokar ‘Yancin Samun Bayanai, yana mai yi wa mahalarta taron fatan samun horo mai amfani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here