Home Labarai Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun Kirsimeti da sabuwar Shekara

Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun Kirsimeti da sabuwar Shekara

0

Gwamnatin tarayyar Najeriya, ta bayyana ranakun 25 da 26 ga watan Disamban bana da kuma 1 ga watan Janairun baɗi, a matsayin ranar hutun bikin Kirsimeti, da ranar rarraba kyautuka da kuma Sabuwar Shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar a Abuja.

Ministan ya taya mabiya addinin Kirista a Najeriya da ma sauran sassan duniya murnar bikin Kirsimeti, tare da taya dukkan ‘yan Najeriya barka da shigowar Sabuwar Shekara.

Ya bukaci Kiristoci da su yi tunani kan darussan ƙauna, zaman lafiya, tawali’u da sadaukarwa da aka nuna ta haihuwar Annabi Isa Almasihu, yana bayyana waɗannan dabi’u a matsayin ginshiƙai masu muhimmanci wajen haɗin kan ƙasa, juriya da zaman lafiya.

Haka kuma, Ministan ya kuma ƙarfafa dukkan ‘yan ƙasa da su yi amfani da wannan lokacin bukukuwa wajen yin addu’a domin zaman lafiya, tsaro da ci gaban ƙasar, tare da tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen bunƙasa ƙasa da ƙarfafa haɗin kai.

Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su kasance masu bin doka, masu kula da tsaro, tare da yin bukukuwan cikin tsari da hankali, yana mai kira ga haɗin kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da hutun bukukuwa ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Haka kuma, ministan ya yi wa ‘yan Najeriya fatan murnar Kirsimeti da kuma Sabuwar Shekara cikin kwanciyar hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here